Jump to content

User:Abubakarfarouq1

From Wikipedia, the free encyclopedia

LITTATTAFAN TASKAR TATSUNIYOYIN HAUSA SUN SAMI TAGOMASHI:

ZA A JUYA SU ZUWA AJAMI

A ranar Juma'a 28 ga watan Mayu na shekarar 2010 ne aka sanya hannu a kan yarjejeniyar juya wasu labaran da ke cikin littattafan TASKAR TATSUNIYOYI na Dr. Bukar Usman OON, zuwa rubutun Ajami, a matsayin littafi, wanda za a hada Hausar Boko da kuma Ajami a waje daya, wato in an karanta rubutun Ajami sai kuma a karanta Hausar Boko a gefe da gefe. An yi wannan yarjejeniya bayan tattaunawa a Tahir Guest Palace da ke unguwar Nasarawa GRA da ke jihar Kano Nijeriya da misalin karfe 4.00 zuwa 6.15 na yamma. An yi wannan yarjejinya ne tsakanin kamfanin Gidan Dabino International, da ke Nijeriya da kamfanin Editions Gashingo da kuma EIRENE Sahel da suke a Yamai ta kasar Nijar.

Mallam Abdou Bako shi ya sanya hannu a madadin kamfanin Gashingo. Sai kuma Mr. Thomas Buttner, Bajamuse, ya sa hannu a madadin kungiyar EIRENE Sahel. Ado Ahmad Gidan Dabino, shi ne wanda ya sanya hannu a madadin marubuci Dr. Bukar Usman da kuma kamfanin Gidan Dabino International. Labaran da aka zaba za a buga su ne kamar haka: